Romans 15

1Mu da muke da ƙarfi ya kamata mu yi haƙuri da kāsawar marasa ƙarfi ba kawai mu gamshi kanmu ba. 2Ya kamata kowannenmu yǎ faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa domin kuma yǎ gina shi. 3Gama ko Kiristi ma bai gamshi kansa ba, amma kamar yadda yake a rubuce cewa: “Zage-zagen da waɗansu suka yi maka, duk sun fāɗo a kaina.”
Zab 69.9
4Gama duk abin da aka rubuta a dā an rubuta ne domin yǎ koya mana, don ta wurin jimrewa da kuma ƙarfafawar Nassosi mu kasance da bege.

5Bari Allah mai ba da haƙuri da kuma ƙarfafawa yǎ ba ku ruhun haɗin kai da juna yayinda kuke bin Kiristi Yesu, 6don da zuciya ɗaya da kuma baki ɗaya kuke ɗaukaka Allah da kuma Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi.

7Ta haka sai ku karɓi juna kamar yadda Kiristi ya karɓe ku, don a yabi Allah. 8Ina dai gaya muku cewa Kiristi ya zama bawan Yahudawa a madadin gaskiyar Allah, don yǎ tabbatar da alkawaran da aka yi wa kakannin kakanninmu 9domin Alʼummai su ɗaukaka Allah saboda jinƙansa, kamar yadda yake a rubuce:

“Saboda haka zan yabe ka a cikin Alʼummai;
zan rera waƙoƙi ga sunanka.”
2Sam 22.50; Zab 18.49

10Ya kuma ce,

“Ku yi farin ciki, Ya Alʼummai, tare da mutanensa.”
M Sh 32.43

11Da kuma,

“Ku yabi Ubangiji, dukanku Alʼummai,
ku kuma rera masa yabo, dukanku mutanen duniya.”
Zab 117.1

12Kuma Ishaya ya ce,

“Tushen Yesse zai tsiro,
wanda zai taso yǎ yi mulkin alʼummai;
Alʼummai za su sa bege a gare shi.”
Ish 11.10

13Bari Allah na bege yǎ cika ku da matuƙar farin ciki da salama yayinda kuke dogara gare shi, domin ku yalwata cikin bege ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.

Bulus Mai Hidima ga Alʼummai

14Ni kaina na tabbata, ʼyanʼuwana, cewa ku kanku kuna cike da kirki, cikakku cikin sani da kuma ƙwararru don yin wa juna gargaɗi. 15Na rubuta muku gabagaɗi a kan waɗansu batuttuwa, don in sāke tuna muku su, saboda alherin da Allah ya ba ni 16in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Alʼummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Alʼummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

17Saboda haka ina taƙama cikin Kiristi Yesu a cikin hidimata ga Allah. 18Ba zan yi karambani in faɗi kome ba sai dai abin da Kiristi ya aikata ta wurina a jagorantar da Alʼummai su yi biyayya ga Allah ta wurin abin da na faɗa da kuma aikata 19ta wurin ikon alamu da ayyukan banmamaki, da kuma ikon Ruhu. Ta haka daga Urushalima har yǎ zuwa kewayen Illirikum, na yi waʼazin bisharar Kiristi. 20Labudda, burina shi ne in yi waʼazin bishara inda ba a san Kiristi ba, don kada yǎ zama ina gini ne a kan tushen da wani ya kafa. 21Sai dai kamar yadda yake a rubuce:

“Waɗanda ba a faɗa musu labarinsa ba za su gani,
waɗanda kuma ba su ji ba za su fahimta.”
Ish 52.15

22Wannan ne ya sa sau da yawa aka hana ni zuwa wurinku.

Shirin Bulus Yǎ Ziyarci Roma

23Amma yanzu da babu sauran wurin da ya rage mini in yi aiki a waɗannan yankuna, da yake kuma shekaru masu yawa ina da marmari in gan ku, 24ina shirin yin haka in na tafi Sifen. Ina fata in ziyarce ku yayinda nake wucewa don ku raka ni can, bayan na ji daɗin zama tare da ku na ɗan lokaci. 25Yanzu kam, ina hanyata zuwa Urushalima don in kai gudunmawa ga tsarkaka a can. 26Gama Makidoniya da Akayya sun ji daɗin yin gudunmawa domin matalautan da suke cikin tsarkakan da suke a Urushalima. 27Sun kuwa ji daɗin yin haka, gama ya zama kamar bashi ne a gare su. Da yake Alʼummai sun sami rabo cikin albarkun ruhaniyar Yahudawa, ya zama musu kamar bashi su ma su taimaki Yahudawa da albarkunsu na kayan duniya. 28Saboda haka in na kammala wannan aiki na kuma tabbata cewa sun karɓi wannan amfani, zan tafi Sifen in kuma ziyarce ku a hanyata. 29Na san cewa saʼad da na zo wurinku, zan zo ne cikin yalwar albarkar Kiristi.

30Ina roƙonku ʼyanʼuwa, saboda Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma saboda ƙaunar Ruhu, ku haɗa kai tare da ni cikin famata ta wurin yin adduʼa ga Allah saboda ni. 31Ku yi adduʼa don in kuɓuta daga hannun marasa bi a Yahudiya don kuma gudunmawar da nake kaiwa Urushalima ta zama abar karɓa ga tsarkaka a can, 32don da yardar Allah, in iso wurinku da farin ciki in kuma wartsake tare da ku. 33Allah na salama yǎ kasance tare da ku duka. Amin.

Copyright information for HauSRK